Featured
Matasa Sun Tuɓe Ɓarawon Doya Haihuwar Uwarsa A Abuja
Al’ummar gari sun tuɓe wani mutum haihuwar uwarsa, saboda kama shi yana satar doya a wata gona a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
An yi wa mutumin wannan ɗanyen hukunci ne bayan an kama shi a karo na biyu a wata gona da ke yankin Kango a Ƙaramar hukumar Kuje.
Wani mazaunin yankin, Bamaiyi Joshua, ya ce a yammacin ranar Litinin ne aka kama ɓarawon doyar a gonar wani dattijo mai suna Ishaya.
Ya ce a kwanakin baya Dattijo Ishaya ya taɓa kama mutumin yana tona doya daga gonar, amma mutumin ya ba shi haƙuri da cewa yunwa ce ta sa shi aikata hakan, shi kuma ya yafe masa.
Bamai yi ta ce, “Ranar Litinin ɗin nan kuma mutumin ya sake dawowa gonar da buhu yana satar doya da masara.
“Amma ya yi rashin sa’a, wani manoma ya gan shi ya sanar da mai gonar.
“Kafin ’yan banga su zo su tafi da shi, mutane sun riga sun lakaɗa mishi duka sun yi masa tsirara.”
