Featured
Mamakon ruwan sama yayi sanadin rayukan mutane da dama
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka samu a ranar juma’ar da ta gabata, ya yi sanadin rayukan mutane tare da jikkata wasu da dama.
Rahotanni da wadansu fefen bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na zamani na nuni da yadda ruwan ya yi awan gaba da dukiyoyin al’ummar garin Maraɗi da kewaye dake Jamhuriyar Nijar.
Kazalika ambaliyar da mazauna garin ke cewa ba a taba ganin irin ta ba a tarihi ta yi sanadiyyar lalacewar hanyoyi da rubtawar gidaje masu tarin yawa.
