Featured
Duk da ƙarin kuɗin shigar da Najeriya ke samu, akwai sauran jan aiki – Masana
Masana harkokin kuɗi da na tattalin arziki sun bayyana wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa ƙaruwar kaso 3.19 na kuɗin shigar Najeriya a zango na biyu na 2024 ya gaza fito da haƙiƙanin halin da ƴan Najeriya ke ciki.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ƙiddiga ta Najeriya (NBS) ta sanar a ranar Litinin cewa, kuɗin shigar Najeriya ya ƙaru da kaso 3.19 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2024, wanda ya ɗara da kaso 2.98 cikin 100 a zangon farko.
A cewar rahoton NBS, ɓangaren kamfanoni da ayyuka sun ba da gagarumin gudunmawa wajen ci gaban kuɗin shigan a zango na biyun.
Ɓangaren ayyukan yau da kullum ya ba da kaso 58.76 na kuɗaɗen shiga, inda ɓangarorin da ba na mai ba suka kawo kaso 94.30, yayin da kuma bangaren mai ya kawo kaso 5.70 a zango na biyun.
Duk da wannan ci gaban da kuɗin shigar ƙasar ya samu, masana tattalin arziki sun yi tambayar mene ne ya sanya har yanzu talakawan Najeriya ba su ga tasirin ƙarin da aka samu ba.
