Featured
Tinubu Ya Karawa Babban Sufeton Ƴan Sanda Wa’adin Mulki
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙarawa Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, wa’adin Shekara uku ma’ana zuwa 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, ne ya bai wa Babban Sufeton ‘yan sandan takardar ƙara masa wa’adin a ranar Litinin 02 ga Satumba, 2024.
A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta yi garambawul ga dokar ‘yan sanda ta 2020, ƙarƙashin sashe na 8 wadda ta ci karo da ƙarawa ma’aikacin gwamnati wa’adin aiki bayan shekara 35, ko kuma bayan kaiwa shekara 60 a raye.
Sai dai Egbetokun wanda aka naɗa IG a watan Yunin 2023, zai cika shekara 60 ne a gobe Laraba 4 ga watan Satumba.
