Connect with us

Featured

Yobe: Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Tayi Alla -Wadai Da Harin Mafa

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, yayi Alla-wadai da harin baya bayan nan da aka kai kauyen Mafa a karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran gidan gwamnatin jihar Ismaila Misilli, ya fitar a yau Laraba 04, ga Satumba 2024. Gwamnan ya bayyana harin a matsayin rashin kyautawa wanda ya haifar da tsoro da firgici ga mazauna kauyen.

Gwamnan ya yaba da kokarin da jami’an tsaro suke yi wajen ganin sun dakile aiyukan yan ta’adda, sai da ya bukaci a kara kokari wajen gano wadanda suke da hannu a wannan ɗanyen aiki, ” Ina kira ga jami’an tsaro su riɓanya kokarin su akan wanda suke yi, kuma wannan abu bai kamata ya tafi a banzai ba, dole ne a hukunta duk wanda suke da hannu a lamarin “, a cewar Yahya.

Gwamnan ya mika sakon jajantawa na kungiyar gwamnonin arewa ga gwamnatin Jihar Yobe, da iyalan wadanda lamarin ya shafa, suna masu rokon Allah ya gafarta wa wadanda suka mutu yayin harin, da kuma nemqn sauki ga wadanda suka jikkata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet