Featured
Akwai yiwuwar tashin farashin kayayyaki a Najeriya – MAN
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya (MAN), ta ce karin kudin man fetur da aka yi a ranar Talata 03 ga Satumba, 2024, zai iya haddasa tashin farashin kayayyaki a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar masana’antu ta Najeriya (MAN), Segun Ajayi-Kadir ne ya bayyana hakan a jiya Laraba 04 September.
Ajayi yace, “Yayin da farashin mai ya tashi, kudaden da mutane ke kashewa zai karu a fannonin sufuri da makamashi, wanda hakan zai rage kudaden da suke samu.”
Ya kara da cewa wannan lamarin zai fi shafar kananan masana’antu, saboda kudaden da suke juyawa ba su taka kara sun karya ba.
Kadir ya kuma bayyana cewa ba abin mamaki bane don farashin man fetir ya tashi a Najeriya, domin dama farashin fetir ya tashi a fadin duniya.
