Featured
Kano: Kotu ta tisa ƙeyar wani alƙalin bogi zuwa gidan gyaran hali
Wata kotun Musulunci dake unguwar kurna a karamar hukumar fagge a jihar Kano, ta tisa ƙeyar wani alƙalin bogi zuwa gidan gyaran hali.
Dubun alƙalin bogin ta cika ne bayan da ya gabatar da kansa a matsayin alkali daga Jihar Jigawa a gaban Kotun, lokacin da yaje neman belin wasu mutane biyu, wadanda ake zargi da laifin damfara da cin amana.
Kotun ta amince da ba shi belin mutanen, akan sharadin zai kai jami’an kotun zuwa gidan sa, sai dai kuma nan take yaki amincewa da bukatar alkalin, bayan an tsananta bincike ne aka gano ma’aikacin shari’a ne, amma bai taɓa zama alkali ba.
Bayan an gurfanar da shi ya amsa laifinsa, sai dai ya roki alkalin kotun ya yi masa sassauci.
Mai Shari’a Khadi Umar Lawan Abubakar, ya bada umarnin tsare shi a gidan gyaran hali zuwa ranar 23 ga watan Satumba, 2024 domin ci gaba da shari’ar.
