Featured
Ku Shirya Wa Matsalar Ƙarancin Man Fetur A Najeriya – NNPCL
An shawarci yan Najeriya su sake shiryawa matsalar karancin man fetur, biyo bayan tashin farashin mai na baya bayan nan.
Mataimakin Shugaban kamfanin NNPCL, Adedapo segun, ne ya bayyana hakan ta cikin wani shiri na gidan talabijin na Arise TV daya gabatar a yau Alhamis 05 ga watan Satumba.
Segun yayi wannan gargadi ne a dai dai lokacin da yan Najeriya suke cikin mawuyacin hali sakamakon tashin farashin man fetir na baya bayan nan.
Ya kuma kara da cewa, akwai bukatar kirkirar kasuwar bai daya don samar da daidaitaccen farashi da kuma saukin rarrabashi a fadin Najeriya.
