Connect with us

Featured

Za mu yi gaskiya da adalci a zaɓen ƙananan hukumomi – Gwamnan Sokoto

Yayin da ake daf da gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin Jihar Sokoto, gwamnan jihar Ahmed Aliyu, ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa zata gudanar da zabe na gaskiya da adalchi a dukkan kananan hukumomi 23 na jihar.

Gwamnan ya kuma shawarci jamiyyar adawa ta PDP ta shiga a dama da ita a zaben da za’a gudanar a ranar 21 ga Satumban da muke ciki.

Gwamnan yayi wannan kira ne a jiya Lahadi 08 ga Satumba, 2024. Lokacin da yake jawabi ga dandazon magoya bayan jamiyyar APC na kananan hukumomi takwas, dake yankin Sokoto ta gabas, waɗanda suka haɗu a Goronyo, don kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi da za ayi a jihar.

“Gwamnatin da ta shude ta PDP itace ta naɗa wadannan Shugabannin na hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar sokoto, kuma ban canza komai ba da nazo”.

“Bansan meyasa jamiyyar PDP take tsoron shigawannan zaben da hukumar SIEC ta shirya ba”, a cewar sa.

A karshe Gwamna Aliyu ya bawa jam’iyyun adawa tabbacin cewa hukumar zaben Jihar Sokoto zata gudanar da zabe na gaskiya da adalchi a fadin Jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet