Featured
Dangote Ya Musanta Siyarwa NNPC Fetur A kan 898
Rukunin kamfanin Dangote ya musanta maganar baya bayan nan da mai magana da yawun kamfanin man fetur na kasa NNPC, Olufemi Soneye yayi na cewa kamfanin ya siyar wa da NNPC fetur akan N898 duk lita.
A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a yammacin jiya Lahadi 15, Satumba 2024. Babban jami’in hulɗar jama’a na rukunin kamfanin Dangote Anthony Chiejina, ya bayyana hakan a matsayin ɓata suna da nufin rage martabar ci gaban da aka samu wajen magance matsalar makamashi ta dindindin a Nijeriya.
Bayanin hakan ya biyo bayan wani rahoto da yake ta yaduwa na cewa NNPCL Ya sayi fetur a matatar Dangote akan N898 duk lita.
Kamfanin ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar, su kuma jira sanarwa daga kwamitin siyar da ɗanyen mai ga manyan matatun mai na cikin gida, wanda zai fara aiki daga 1 ga Oktoba, 2024. Chiejina ya bayyana cewa, ɗanyen man da kamfanin ke amfani da shi yanzu haka an saye shi ne da dala kuma ana siyar da shi ga NNPCL da dala, wanda duk da haka an samar da ragi mai yawa idan aka kwatanta da man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
A karshe sanarwar ta ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, kamfanin na da niyyar tabbatar da wadatar mai mai inganci a faɗin ƙasar, da nufin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man fetur da aka daɗe ana fama da ita.
