Featured
Kada ku karaya, ku cigaba da marawa gwamnatin Tinubu baya
Shugaban Jamiyyar APC na Kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya roki yan Najeriya su cigaba da marawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, saboda kokarin da gwamnatin take wajen ganin ta farfado da tattalin arziki a fadin kasar.
Ganduje ya fadi haka ne a jiya Lahadi 15 ga Satumba, ta cikin wata sanarwa da ya fitar don taya al’ummar musulmi murnar bikin maulidi.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmi su yi koyi da kyakkyawar rayuwa, tare da kwaikwayon kyawawan halaye na Annabi Muhammad S.A.W. Shugaban na Apc yace Najeriya tana bukatar addu’o’i, tare da goyon bayan yan kasa baki daya musamman a irin wannan lokaci.
Ganduje yace, ” A wannan lokaci da muke ciki, ina rokon yan Najeriya su cigaba da nuna goyon bayan su ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sakamakon kokarin da yake wajen ganin ya farfado da tattalin arziki a kasar nan.
“Dukkan yan jam’iyya ya kamata suyi amfani da wannan lokaci na maulidi wajen biyayya ga koyarwar Annabi Muhammad SAW, tare da yin aiki gaba daya don gina kasarmu da kuma tabbatar da zaman lafiya.
“Annabi Muhammad SAW shine babban misali wajen jagoranci, sakon sa na Musulunci yana dauke da jinkai a ciki. A yanzu da muke bikin murnar zagayowar rananr haihuwar sa, dole ne mu tabbatar da cewa muna bin tsari na gaskiya da adalchi kamar yadda ya koyar”. Inji Ganduje.
