Connect with us

Featured

UAE ta tallafawa waɗanda ambaliya ta shafa a Najeriya

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ba da tallafin kayan jin ƙai mai nauyin ton 50 ga Najeriya, don taimaka wa waɗanda suka yi asarar gidaje sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a kwanakin baya.

An mika kayan agajin ga jami’an gwamnati na Nijeriya da hukumar kula da agajin gaggawa (NEMA), ma’aikatar harkokin waje, da Ofishin mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Jakadan UAE a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya miƙa wannan tallafi a madadin Shugaba Sheikh Mohamed Al Nahyan, inda ya jaddada aniyar UAE na tallafa wa ƙasashen da ke fuskantar iftila’i.

A nasa jawabin, Dr. Ahmed Dunoma, Sakatare Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, ya gode wa UAE a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa akwai alaka mai kyau tsakanin kasashen biyu.

Babbar Daraktar NEMA, Zubaida Umar, ta kuma nuna godiya ga UAE, inda tace tallafin zai taimaka wajen ci gaba da ƙoƙarin taimaka wa al’ummomin da ambaliyar ta shafa wajen rage raɗaɗi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet