Featured
Direbobi na buƙatar nutsuwa kafin fara tuƙi – FRSC
Kwamandan Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa reshen Jihar Ogun, Akinwumi Fasaki, yace akwai bukatar matuka ababen hawa su tabbatar sun samu isashshen hutu kafin fara kowace irin tafiya.
A cikin wata sanarwa da kwamandan ya fitar a yau Talata 17 ga Satumba a garin Abeokuta, ta hannun mai magana da yawun sa, ya bukaci direbobi su tabbatar sun samu hutu gamsashshe, domin gudanar da tuki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
“Ya kamata direbobi su samu hutu na minti 15 zuwa 30 duk lokacin da sukayi tuki na tsawon awa hudu”, a cewar sa.
Jaridar dillanci labaru ta Najeriya (NAN), ta rawaito cewa Fasaki ya bada wannan shawara ne biyo bayan wani hatsari da ya afku a jiya litinin a jihar, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, tare da jikkatar akalla mutane takwas.
