Featured
APC ta lashe zaɓen gwamna a jihar Edo
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar jamiyyar APC, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Edo da aka gabatar a ranar Asabar.
Okpebholo ya samu nasara ne bayan samun kuri’u 291,667, wanda hakan ya bashi nasara akan abokin takarar sa na jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, wanda ya samu kuri’u 247,274.
Dan takarar jamiyyar Labour Party, Olumide Akpata, shine yazo na uku bayan samun kuri’u 22,761.
“Monday Okpebholo, na jam’iyyar APC bayan ya cika dukkan sharudan da doka ta tanada, shine ya lashe wannan zabe,” a cewar baturen zaben Prof. Faruk Kuta, wanda ya sanar da hakan da misalin karfe 09:27 na daren ranar Lahadi 22 ga watan Satumba, 2024.
