Featured
Gwamnatin Kano ta ciyo bashin Biliyan 177.4 don gyaran gidan ruwa na tamburawa
Gwamnatin Jihar Kano ta samu bashin Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Cigaban Faransa wato French Development Agency domin gyaran gidan ruwa na Tamburawa da kuma inganta samar da wadataccen ruwan sha a fadin jihar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ruwa na jihar, Alhaji Ali Haruna Makoɗa ya wakilta ne ya bayyana hakan a wani taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da aka yi a Kano domin bibiya da tsara aikace-aikace wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato da Enugu da Ondo.
A cewar sa aikin na samar da ruwan sha, yana cikin shirin inganta samar da ruwan sha na ƙasa, wanda ya samu sahalewar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Najeriya.
Injiniya Garba Ahmad Bichi, Manajan Darakta na Hukumar Gidan Ruwa ta Kano ya ce aikin ya ƙunshi sake gina sabon hanyar adanawa da gyara ruwa wanda zai ɗauki lita miliyan 250 a kullum, wanda ya ce zai taimaka matuƙa wajen rage matsalar ƙarancin ruwa a jihar.
