Featured
In Ka Ga Ɗan Siyasa Ko Jami’in Gwamnati Ba Ya Cin Hanci Tabbas Ɗan Baiwa Ne – Ndume
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Tarayya, Muhammad Ali Ndume, ya bayyana yadda cin hanci da rashawa yayi ka-tu-tu a Najeriya.
Ndume, ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Lahadi 29 ga Satumba a Kano, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito.
Sanatan yace cin hanci da rashawa yayi wa Najeriya illa ta yadda za ka ga yan siyasar da suka saci kudi suna alfahari da hakan.
“Babban kalubalen mu a wannan kasa shine cin hanci da rashawa, amma har yanzu babu wata doka da aka yi don ganin an magance hakan a kasar nan. In kaga mutum a kasar nan musamman yan siyasa ko jami’in gwamnati wanda ba dan rashawa ba, to dan baiwa ne mai tsoron Allah, amma a Najeriya ne za ka saci kudi sannan kaje duk inda kakeso ka yawata”.
“A kasar nan ne mutumin da kowa ya san shi jiya bashida ko sisi, amma ƙasa da sati ɗaya sai ya siyi mota goma, yan uwan sa da iyayen sa kuma su yi ta murna suna cewa Allah ne ya bashi”.
A cewar sa, ya taba gayawa wani tsohon shugaban kasar nan akan ayi wata doka game da harkar cin hanci amma yaki.
