Connect with us

Featured

Sarki Aminu Ado Bayero ya jajantawa waɗanda ibtila’in gobarar Kasuwar Kwari ta shafa

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya kai ziyarar jaje ga ƴan kasuwar Kantin, Jim kadan bayan dawowarsa daga ziyarar aiki da yaje Abuja.

Cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran sarkin, Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, ya aikowa jaridar Kakaki24 a ranar Lahadi, yace dubun dubatar masoya da magoya baya ne sukayi cincirundo domin raka mai Martaba Sarkin kasuwar ta Kantin kwari.

Da yake jajantawa wadanda suka gamu da ibtila’in gobarar, Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya mayar da asarar da akayi a kasuwar tareda addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma godewa Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Jami’an tsaro da Kungiyar Yan kasuwar da dai daikun al’uma bisa yadda suka bada dugunmawa wajan tabbatar da kashe gobarar.

Sarkin daga nan sai ya bukaci Yan kasuwa da sauran al’uma su cigaba dayin addu’oi domin kiyayewar afkuwar irin wannan ibtila’i tareda neman samun sassaucin al’amura na rayuwar yau da kullum.

Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yakai ziyarar aiki ne babban Birnin Tarayya Abuja tareda halartar wasu tarurruka, inda daga dawowar sa ne ya zarce domin yin jaje ga Yan kasuwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet