Featured
Kotu ta bai wa KANSIEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi
Babbar kotun jihar kano ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar KANSIEC, damar gudanar da zaben kananan hukumomi wanda aka shirya gudanarwa a ranar asabar 26 ga watan Oktoba 2024.
Babbban Alkalin kotun Mai Shari’a Sanusi Ma’aji, ne ya bada umarnin a yau Juma’a, lokacin da yake yanke hukuncin kan karar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano ta shigar, inda take kalubalantar Jamiyyar APC da wasu jjamiyyu 13.
Mai Shari’a Ma’aji ya bayyana cewa hukumar zabe ta jihar kano tana da damar shiryawa da kuma gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata dama.
Ma’aji ya kuma umarci dukkanin jami’an tsaro dake jihar da su tabbatar sun samar da tsaro yayin zaben kananan hukumomin wanda za a gudanar a gobe Asabar 26 ga Oktoba 2024.
