Connect with us

Featured

Tinubu ya nuna damuwarsa kan halin rashin wuta da al’ummar yankin Arewa ke fama da ita

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa kan halin duhu da ake ciki a arewacin Najeriya sakamakon rashin wuta tsawon mako guda.

Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai Nayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin, ya ce a yanzu Shugaban Ƙasar ne jan ragamar koƙarin kawo ƙarshen rashin wutar wadda ta kawo tsaiko da durƙusar da harkokin tattalin azriki da zamantakwa.

Sanarwar ta kuma cewa Shugaba Tinubu ya nemi ganin Ministan Makamashi Adebayo Adelabu da Babban mai bai wa shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu don tattauna batun.

“Shugaban ƙasar ya umarci Ministan Makamashi da sauran hukumomin da suka dace da su gaggauta aikin dawo da wutar lantarki a dukkan yankinan da abin ya shafa a Arewa.

“Shugaba Tinubu ya yi bakin ciki da rahotannin ɓarna da lalata kayayyakin wutar lantarki da sauran kadarorin al’umma da suka yi sanadin jefa yankin a cikin duhu.

A ganawar da ya yi da Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, wanda ya yi bayani kan kokarin da Kamfanin Samar da Lantarki na Nijeriya ya yi na gyara layukan da suka lalace daga Shiroro zuwa Kaduna, sanarwar ta ce Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin a magance matsalar a mataki na dogon zango.

Shugaba Tinubu ya bukaci injiniyoyin TCN da kada su yi kasa a gwiwa wajen kawo dauki cikin gaggawa ga mutanen da ke bukatar wutar lantarki domin ci gaba da harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki.

Don ganin an ci gaba da aikin farfado da aikin ba tare da tangarda ba, Shugaba Tinubu ya kuma umurci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da ya hada kai da sojoji da sojojin sama domin aikewa da isassun jami’an tsaro da suka hada da jirgin sama domin kare injiniyoyin da ke gyara layin da ya lalace.

Shugaba Tinubu ya roki sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, da sauran shugabannin da su hada kai da hukumomin tsaro domin kare kadarorin jama’a da ababen more rayuwa.

Ya ce gwamnati ba za ta sake lamuntar da gangan a yi zagon kasa da lalata kayayyakin amfanin jama’a ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinovdcasinoholiganbetmarsbahissahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet