Connect with us

Featured

NNPCL Ya Ƙara Farashin Man Fetur A Karo Na Biyu Cikin Wata Guda

Yan Najeriya da dama sun cika da mamaki bayan ganin kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL, ya kara kudin man fetur a jiya Talata 29 ga Oktoba 2024, wanda wannan shine Karo na biyu da kamfanin yayi ƙari cikin makonni uku.

Kamfanin man na kasa ya kara farashin a jiya Talata daga naira 1,030 zuwa 1060 a Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da a Jihar Legas farashin ya koma Naira 1,025 daga 998 a kowacce lita.

Kafin wannan ƙarin, ana sayar da litar man fetur ne a  kan N897 a Abuja, a Legas kuma N885, amma a ranar 9 ga watan Oktoba da muke bankwana da shi aka ƙara na Legas zuwa N998, na Abuja kuma zuwa N1,030.

Ķarin kudin na zuwa ne duk da fara aikin Matatar Man Ɗangote, wadda ake tunanin za ta kawo sauki da wadatuwar man a ƙasar.

Tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye Tallafin mai a watan mayun 2023, NNPCL ya ƙara kudin fetir daga 184 zuwa 1,025 a Jihar Legas.

Masana dai na ganin wannan wani mataki ne da zai kara jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali, dama tuni wasu suka ajiye ababen hawan su saboda tsadar farashin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet