Featured
Za a fara rigakafin Kyandar Biri a Najeriya
A yau Litinin 18 ga Nuwamba 2024, ne za a fara allurar riga-kafin ƙyandar biri a wasu jihohi bakwai a Najeriya, wanda hakan zai sa Najeriya ta zama kasa ta uku da za ta yi riga-kafin bayan Rwanda da Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.
Ma’aikatar lafiya ta ce za a fi mayar da hankali ne a kan ma’aikatan lafiya da sauran rukunan jama’a da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Tun a watan Agusta Najeriya ta karɓi alluran riga-kafin na farko da aka bai wa Afirka, wanda kuma a wannan watan ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya
Amurka ta bai wa Najeriya kwalaban allurar sanfurin Jynneos (MVA), guda 10,000
Tun daga farkon shekarar nan rahotanni sun tabbatar da mutum 118 a jihohi 28 daga cikin 36, da kuma Abuja ne suka kamu da cutar a Najeriya, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta sanar.
Hukumar yaki da bazuwar cutuka ta Najeriya ta ce, zuwa yanzu a wannan shekara daga watan Oktoba, 27, akwai mutane 1,442 da ake zargin sun kamu da cutar daga jihohi 36 da kuma Abuja.
