Featured
Dokar gyaran haraji ba za ta talauta yankin arewa ba – Fadar Shugaban Ƙasa
Fadar Shugaban Kasa ta musan ta zargin cewa, kudirin dokar gyaran haraji da Shugaba Tinubu, ya aikewa Majalisar dokokin kasar nan zai talauta yankin Arewa, Kazalika ta ce zancen cewa Jihar Legas da Rivers su za su amfana da tsarin wannan shaci-fadi-ne kawai.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 02 ga Disamba, 2024. Ya ce manufar gyaran harajin shine a inganta rayuwar yan Najeriya gaba daya.
Martanin ya biyo bayan zargin da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi, inda yace dokar harajin za ta amfanar da Jihar Lagos da Rivers ne kawai.
“Wannan ƙuduri ba zai azurta jihar Lagos ko Rivers ba, kuma ba zai sa wasu sassan ƙasar su ƙara talaucewa ba kamar yadda ake yayatawa”, a cewar Onanuga.
Ya kuma bayyana cewa, babu wani sashe na sabon ƙudurin haraji da aka gabatar ga majalisa domin samun amincewa da ya tanadi soke wasu hukumomi irin su TETFUND, da NASENI, da kuma NITDA.
