Connect with us

Featured

EFCC ta yi kwace mafi girma a tarihi, inda ta ƙwace gidaje 753 mallakin wani jami’in gwamnati a Abuja

Kotu ta kwace wasu rukunin gidaje 753, daga wani tsohon jami’in gwamnati da ake zargi da almundahana a kan kudaden al’umma a Abuja.

Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ne ya ba da umarnin kwace gidajen a ranar Litinin 02 ga Disamba, 2024. A lokacin da ake cigaba da shari’ar da Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta gurfanar da wanda ake zargin.

“Wanda ake zargin ya Mallaki wadannan gidaje ba bisa ka’ida ba, kuma ya kasa kawo dalilan da zai iya gamsar da kotu, don haka kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya wadannan kadarori”, a cewar Mai Shari’a Onwuegbuzie.

An kwace gidajen ne wadanda suke a yankin Cadastral Zone C09, Lokogoma a Birnin Abuja, wannan kuma shi ne kwacen kadarori mafi girma a lokaci guda da hukumar EFCC ta yi nasarar yi tun da aka kafa ta shekara 21 da suka gabata.

Shugaban Hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede, yace, wannan wata babbar nasara ce a kokarin da suke na yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet