Connect with us

Featured

Yansanda sun kama barawon mota a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu nasarar cafke wani da ake zargin ya sace wata karamar mota kirar Rav-4 mini jeep mai launin toka mai lamba YAB 881 JK Abuja.

Da yake tabbatar da samun nasarar, Mai Magana da yYawun Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin 06, January 2025. Ya ce, “A ranar 28 ga watan Disamba 2024, da misalin karfe 5:00 na yamma, tawagar ‘yan sandan da ke yaki da satar motoci sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), ta gano motar kirar Rav-4.

A cewar sanarwar, motar mai launin toka-toka, mai lamba, YAB 881 JK, Abuja, an gano ta ne a yayin wani sintiri a Kwanar Ungogo da ke karamar hukumar Ungogo a jihar.

“Binciken farko-farko ya sa aka kama babban wanda ake zargin, Bala Sani, mai shekaru 40 a Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

A cewar sanarwar, “an kama wanda ake zargin ne a ranar 4 ga Janairu, 2025, a mahaifarsa da ke Kwado Quarters, Karamar Hukumar hukumar Katsina.

A yayin binciken farko, wanda ake zargin ya amsa laifin hada baki da wani mutum don satar motar kirar Rav-4 daga Zaria, jihar Kaduna.

Ya kara da cewa shi ne da kansa ya tuka motar zuwa Kano da nufin siyar da ita, amma da ya fahimci akwai jami’an ‘yan sanda kusa da Junction na Ungogo, sai wanda ake zargin ya yi gaggawar barin motar ya tsere zuwa garinsu.

“A halin yanzu dai karamar motar jeep din da aka gano tana hannun hukumar, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu”, in ji Kiyawa.

Rundunar ta kuma bukaci mai motar da ya kai rahoto Ofishin Hulda da Jama’a ’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ko kuma ya tuntubi wannan lambar 08067885568 da kuma shaidar cewa shi ne mamallakin motar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet