Featured
Gwamnatin Bauchi za ta kashe miliyan 170 don siyan Janareta ga ofishin SSG
Gwamnatin jihar Bauchi ta gabatar da kudirin naira miliyan 400 a cikin kasafin kudinta na 2025, don siyan kwamfutoci guda shida ga ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma yi kasafin Naira biliyan 1 don siyan filaye don gina ofisoshi da gidaje, kazalika gwamnatin za ta kashe Naira miliyan 170, don siyan janareta don samar da wutar lantarki ga ofishin sakataren gwamnatin.
Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Ibrahim Musa, ya caccaki shirin gwamnatin, inda ya bayyana su a matsayin abubuwan da ba su kamata ba, duba da yanayin matsin tattalin arziki da kasar nan ke fama da shi a halin yanzu.
