Featured
Tinubu Ya Jaddada Muhimmancin Bin Doka Don Tabbatar Da ɗorewar Zaman Lafiya
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin da ke akwai kan bin doka da oda a Jihar Ribas domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da ci gaba.
Tinubu ya faɗi hakan ne a yayin da yake jawabi ga shugabannin siyasar yankin Kudu-maso-Kudu a ranar Talata a Abuja, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasar na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.
A yayin taron da wakilai da shugabannin Neja Delta ƙarƙashin ƙungiyar Pan-Niger Delta Forum (PANDEF), shugaban Kasar ya nanata cewa mutunta ɓangaren shari’a na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradiyya da samar da zaman lafiya.
Ya shawarci shugabannin da su kasance masu zurfin tunani da rashin son-kai da kuma mai da hankali kan hangen nesa na ceto yankin, a siyasance da tattalin arziki, ta hanyar dagewa wajen mutunta dokokin shari’a na kundin tsarin mulkin kasar.
“Ina tare da ku da yardar Allah, ina godiya da goyon bayanku, addu’o’inku da damuwarku. Ba zan iya yin ƙorafi ba, ni na yi yakin neman zaben wannan mukami kuma na nemi aikin, dole ne in yi shi da zuciya daya, duk runtsi. Zan tabbatar mun cim ma alkawuranmu da manufofinmu,” in shi Shugaban Ƙasar.
“Na dade ina bibiyar rikicin Rivers”
Tinubu ya shaida wa wakilan ƙungiyar PANDEF cewa ya daɗe yana bibiyar rikicin Jihar Rivers, inda ya yi kira ga shugabannin da su zama masu bin dokokin kundin tsarin mulki.
“Tabbas Neje Delta ita ce kazar da ke yi mana ƙwan zinare. Dole mu kula da kazar nan; in ba haka ba za mu rasa ƙwan zinaren. Na samu saƙonku da damuwarku, musamman kan Jihar Rivers, na daɗe ina bibiyar batun. Na ga rikicin ya dade yana ci kafin na shiga tsakani.
“Mun cim ma yarjejeniya, a rubuce, kuma duka bangarorin biyu sun sanya hannu.”
Shugaba Tinubu ya ce dole ne masu ruwa da tsaki su yi sadaukarwa domin jihar ta ci gaba ta hanyar amincewa da bin Kundin Tsarin Mulki.
Ya kuma buƙace su da su bi umarnin da kotu ta bayar a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
