Featured
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Shugabanin Tsaron Kasar Nan A Villa
Shugaba Bola Ahmad Tinubu a ranar Talatar nan ya gana da hafsoshin tsaro karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa a fadar Aso Villa dake Abuja.
Sauran wadanda suka laraci ganawar sun hadarda Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da Darakta Janar na Hukumar tsaron farin kaya DSS, Oluwatosin Ajayi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; da shugaban masu rinjaye, sai Opeyemi Bamidele; wanda daga baya ya shiga taron da aka gudanar a ofishin shugaban kasa.
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas; da mataimakinsa, Ben Kalu suma an gansu a wurin taron.
Ba a bayyana makasudin taron ba ha zuwa lokacin hada labarin amma mai yiwuwa bai rasa nasaba da matsalar tsaron da Kasar nan take ciki.
