Connect with us

Featured

Matatar Man Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Fetur Da Naira

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man da Naira na wucin gadi.

Kamfanin Dangote ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Larabar nan da rana.

A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka.

“Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira.

“Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar.

Kamfanin na Dangote ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da sayar da man fetur.

Haka kuma ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ya jaddada cewa tsarinsa yana da inganci kuma ba a samu wata matsala ba.

Matatar ta Dangote ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da mai a Naira da zarar ta samu ɗanyen mai da aka sayar mata a Naira daga kamfanin NNPC.

“Muna nan daram wajen yi wa kasuwar Najeriya hidima, kuma za mu dawo da sayar da mai a Naira da zarar mun samu kaya,” in ji sanarwar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet