Featured
Rivers: Majalisar Dattawa Ta Bi Sahun Ta Wakilai Kan Dokar Ta-ɓacin
Kamar Majalisar Wakilai, Majalisar Dattawa ma ta amince da dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar Ribas, tare da yin amfani da karfin ikonta na kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa kwaskwarima na 1999.
Amincewar ta bai wa shugaba Tinubu ikon aiwatar da matakan gaggawa yayin da yake ba da umarnin sake duba lamarin a kowane lokaci, amma bai wuce watanni shida ba.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, majalisar dokokin kasar ta kuma kafa wani kwamitin hadin gwiwa na majalisun biyu domin sa ido kan yadda ake tafiyar da al’amuran jihar ta Ribas a cikin wa’adin na gaggawa.
Bugu da kari, majalisar dattijai ta yanke shawarar kafa kwamitin sasantawa da ya kunshi fitattun ‘yan Najeriya don taimakawa wajen warware rikicin siyasar jihar.
A ranar Talata ne shugaban Kasa Tinubu ya yi amfani da karfin ikonsa a Rivers, inda ya ayyana dokar ta baci a jihar. Ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara; Mataimakiyarsa Ngozi Odu da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon watanni shida tare da nada wani shugaba daya tilo da zai jagoranci jihar a wani mataki da ya janyo cece-kuce.
Masana harkokin shari’a, gwamnoni, da fitattun ‘yan Najeriya irinsu Atiku Abubakar, Peter Obi, sun yi Allah-wadai da wannan mataki, suna neman a sauya tsarin.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ninka karfin matakin na Tinubu inda ta ce ana bukatar zaman lafiya a jihar mai arzikin man fetur.
