Connect with us

Featured

Shugaban Chadi Ya Naɗa Ƙaninsa A Matsayin Sakatarensa

Shugaban Kasar Chadi Mahamat Idriss Deby ya naɗa ƙaninsa a matsayin sakatarensa kamar yadda wani ƙunshin dokar ƙasar da aka wallafa a Larabar da ta gabata ya nuna.

Yanzu haka Daoussa Idriss Deby Itino ya maye gurbin Ahmed Kogri wanda aka kora daga muƙaminsa na Sakataren Shugaban Ƙasa.

Makusantan Daoussa sun bayyana shi a matsayin mutum kamili, mai haƙuri da nutsuwa, yayin da ake ganin ɗarewarsa kan mukamin na Sakataren Shugaban Ƙasa, wata dama ce da ke share masa fagen zama shugaban ƙasa nan gaba.

Gabanin garanbawul ɗin da shugaba Mahamat ya yi, Daoussa ya kasance mataimakin Sakataren Shugaban Ƙasa, inda ya yi aiki a ƙarƙashin Ahmed Kogri da ya gada.

 

Tuni ya fara zartas da ɗimbin ayyukan da ya gada daga tsohon maigidansa kamar yadda wasu majiyoyin sirri suka bayyana.

Wasu bayanai na cewa shi dai Ahmed Kogri ya riga ya kai maƙurarsa a siyasa, yayin da yake ci gaba da shan suka saboda kusancinsa da Faransa.

A ɓangare guda, tun lokacin da Mahamat ya ɗare karagar mulki Chadi, ya yi wa kanin nasa ƙarin girma zuwa muƙamin janar na soji kafin sake ɗaga likafarsa zuwa Sakatarensa na Musamman.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet