Connect with us

Featured

Yadda Martanin Kwankwanso Kan Dokar Ta-ɓaci A Rivers Ya Yamutsa Hazo

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wasu kalamansa kan ‘yan Majalisar wakilai na Kasa da ya ce ‘yan amshin Shata ne su bayan amince wa dokar ta baci a jihar Rivers da suka yi, sun jawo cece-kuce a Najeriya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Sanata Kwankwaso ya ce abin da ‘yan Majalisar suka yi wani abin kunya ne.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ci gaba da cewar matakin ‘yan majalisar ya nuna rashin dattako kuma babbar barazana ce ga dimukuradiyar kasar.

Ya kuma ce abin da Shugaba Tinubu ya yi na dakatar da gwamnan farar hula tamkar gayyato sojoji ne, bayan kokarin da tsohon Shugaba Obasanjo ya yi na killace su a bariki.

Da yawan ‘yan Najeriya ma dai na mamakin yadda ‘yan majalisar wakilai masu shahadar gidan imanin Kwankwasiyya ma suka yi shiru lokacin muhawara kan kudirin, wanda ake ganin kamar su ma sun bi yarima sun sha kida tare kuma da bijire wa ra’ayin madugunsu, domin ya yi gabas sun yi yamma.

Sai dai guda daga wadannan ‘yan majalisu me wakiltar karamar hukumar Gwale a Kano, a majalisar Honorabul Garba Diso ya ce masalahar jihar Rivers suka kalla da kuma kyakkyawar niyyar tabbatar da zaman lafiya a jihar mai arzikin man fetur.

Akwai dai zargi da aka yi na cewar an yi amfani da kudi wajen saye imanin wasu ‘yan majalisun na Najeriya, domin tabbatar da wannan kudiri.

Zargin da muka yi kokarin jin bahasinsa daga dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano, Alhaji Sagir Koki, wanda ya ce zai bayar da amsa, amma kuma shiru har wannan lokaci bai ce komai ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet