Featured
An Samu Girgizar Kasar A Bangkok Da Ke Thaïland Da Myanmar
Girgizar kasa da ta auku a Bangkok babban birnin kasar Thailand ta hallaka akalla mutane uku yayin da wasu gommai kuma suka sami raunuka. Mutane da dama a birnin sun jiwo amon girgizar kasar.
Cibiyar nazarin kimiyyar kasa ta Jamus GFZ ta ce girgizar kasar ta fi karfi a makobciya kasar Myanmar kamar yadda bayanan farko suka nuna.
Ita ma cibiyar nazarin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta kai karfin maki da 7.7 a maunin richter tare da kananan amo da suka biyo baya mai karfin maki 6.4.
An ruwaito samun hasarar rayuka a kasashen biyu Thailand da Myanmar sai dai har yanzu ba a san adadin mutanen da lamarin ya shafa ba.
Firaministan Thailand ya ayyana dokar ta baci a Bangkok yayin da Myanmar ta sanar da dokar ta baci a babban birnin da kuma birni na biyu mafi girma a kasar.
