Connect with us

Featured

Ƴansanda Sun Kama Mutum 14 Da Ake Zargi Da Hannu A Kisan ’Yan Arewa A Jihar Edo

Jami’an ’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo.

Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Kasar nan, Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Shelkwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike.

Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Haka kuma, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere.

Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da umarnin a kamo waɗanda ke da hannu a lamarin.

Ya tabbatarwa da al’umma cewa ’yan sanda ba za su yarda da kisan gilla ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Sufeto-Janar ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su ba da haɗin kai wajen bincike.

Haka kuma, ya gargaɗi mutane kan ɗaukar doka a hannunsu, tare da tunatar da su cewa mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba laifi ne.

’Yan sanda sun kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da kiran su da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani wanda ba su yarda da shi ga hukumomin tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet