Connect with us

Featured

Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Mutane 74 A Ƙasar Nan — NCDC

Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Kasa NCDC ta nuna damuwa kan samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar sanƙarau a ƙasar, inda ta tabbatar da mutuwar mutane 74 tare da wasu 807 da suka kamu da cutar a jihohin ƙasar 22.

Cibiyar ta kuma yi kashedin cewa cutar ta yin ƙamari ne daga watan Nuwamba zuwa Mayu, saboda haka, dole a cigaba da ɗaukar matakan kariya.

Babban darakatn wannan cibiya, Dakta Jide Idris ne ya bayyana haka a wata ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wannan Litinin a Abuja.

Idris ya ce cibiyar ta samar da tsarin ɗaukin gaggawa a musamman jihohin Kebbi, Katsina da Sokoto, inda aka fi samun yawan waɗanda suka harbu da cutar.

A cewarsa, a jihar Kebbi kaɗai an samu mutane 248 da suka kamu da cutar, da 26 da cutar ta kashe tun daga ƙarshen watan Janairu zuwa yanzu.

Ya yi karin bayani akan cutar sanƙarau, inda ya bayyana ta a matsayin cutar mai matuƙar haɗari, wadda ke kama ƙwaƙwalwa da laka, kuma alamominta sun hada da zazzaɓi mai zafi, ciwon kai da amai da kuma sanƙarewar wuya, kuma tana kisa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet