Connect with us

Featured

Dan Wasan Gaba Na Manchester City Haaland Zai Yi Jinyar Mako Bakwai

 

Mai horaswar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi.

Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti 61 da fara wasan bayan ya farke ƙwallo ɗaya, kafin daga bisani City ta doke Bournemouth da ci biyu da ɗaya domin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.

Tun a jiya Litinin ce City ta ce Haaland zai ga ƙwararren likita saboda raunin da ya ji, kuma tana sa ran zai warware ya ci gaba da taka leda a wannan kakar da ake ciki.

Sai dai a yau Talata gabanin wasan da City za ta fafata da Leicester City a Firimiyar Ingila, Guardiola ya sanar da cewa likitocin sun tabbatar da cewa ɗan wasan zai yi jinyar mako biyar zuwa bakwai kafin ya iya dawowa taka leda a Etihad.

A bayan nan dai City na fuskantar cakwakwiyar ’yan wasa da ke fama da jinya, ciki har da Rodri wanda ya lashe kambun gwarzon ɗan wasa ta Balon d’Or a bara.

A yanzu dai City ba ta wani ɗan wasa da zai iya maye gurbin Haaland, amma Guardiola ya ce ƙungiyar za ta ƙarasa kakar wasannin a daddafe a haka kuma za ta jajirce don samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai mai zuwa.

A halin yanzu City mai maki 48 na mataki na biyar a teburin Firimiyar Ingila yayin da ya rage mata wasanni tara da kuma wasan mataki na biyun ƙarshe a Kofin FA da za ta kece raini da Nottingham Forest a wannan wata na Afrilu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet