Featured
Gwamnan Kano Ya Bukaci Nuna wa Duniya Mutanen Da Suka Kashe ’Yan Arewa A Edo
Gwamnan Kano ya karɓi baƙuncin takwaransa na Edo, Monday Okpebholo wanda ya ziyarci jihar domin jajanta wa gwamnati da al’ummar dangane da kashe mafarautan da wasu ’yan sa-kai suka jagoranta a jiharsa.
Da yake sake bayyana takaicinsa, Abba ya buƙaci gwamnan na Edo ya gaggauta gurfanar da waɗanda aka kama kan kisan matafiyan a bainar jama’a.
Abba ya kuma yaba wa yadda Mista Okpebholo ya gaggauta tashi-tsaye kan lamarin da a yanzu har an cafke wasu mutum 14 da ake zargi da aika-aikar.

‘Muna so a nuna wa duniya fuskokin mutanen da aka kama’
Sai dai gwamnan na Kano ya ce “bayan kama su, muna kuma so a yi holensu a bainar jama’a, domin duniya ta ga fuskokin waɗanda suka yi wannan ɗanyen aiki.”
Ya nanata cewa Jihar Kano tamkar wata cibiya ce ta zaman lafiya “saboda haka muna gargaɗin duk ’yan Nijeriya cewa ƙasar nan ta kowa ce.”
Ya buƙaci shugabanni da su haɗa kai wajen ganin ba a sake maimaita irin wannan mummunan lamari ba a ko’ina a faɗin ƙasar, “saboda haka muna kira mahukunta sun ɗauki mataki mai tsauri a kan irin wannan.”
Da yake nasa jawabin, Gwamna Okpebholo ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an bi kadin rayukan da aka kashe, yana mai cewa a halin yanzu tuni an kama wasu mutum 14 da ake zargi kuma za a miƙa su Abuja domin ci gaba da bincike.
Kazalika, ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin Hausawa da duk wasu ƙabilu da ke zaune a jihar ta Edo.
Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa — Gwamnatin Kano
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar Edo.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin saƙonsa na barka da sallah kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi.
Tun a jiya ne daman wasu majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano ta ce ana kuma sa ran karɓar baƙuncin Gwamnan Edo domin jajanta wa gwamnatin da kuma iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
Mahukuntan Edo na tattaunawa da takwarorinsu na Kano kan lamarin
Yanzu haka ana ci gaba da bincike dangane da wannan lamari, kuma tuni aka kama mutane 14 da ake zargi, yayin da ake farautar wasu mutane da dama da suka arce kamar dai yadda Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya ya bayar da umarni.
Gwamnatin Edo ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dangin marigayan, da kuma mahukuntan jihar Kano, lura da cewa mafi yawan ’yan asalin jihar ne, tare da ɗaukar alƙawarin cewa za a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta waɗanda aka sama da laifi.
Bayanan da suka fito fili bayan faruwar wannan lamari, sun tabbatar da cewa mafarautan sun fito ne daga Fatakwal da ke Jihar Ribas a hanyarsu ta zuwa Kano domin yin bukukuwan sallah a cikin iyalansu.
Dole a kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa ’yan Arewa
Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar.
Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.
“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Nijeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.
“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.”
Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”
