Connect with us

Featured

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Sarkin Kano Na 16 Don Yin Bincike

 

Rundunar ‘yan sandan Kano ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, domin yin bincike kan wani lamari da ya faru a yayin bikin Sallah ta bana.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 30 ga wata. Maris, 2025, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani Usman Sagiru, mai shekaru 20, dan unguwar Sharifai Quarters, bisa zargin kisan kai ga wani jami’in banga a tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi II bayan sallar idi.

Hakazalika rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin tare da mika goron gayyata ga Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin yi masa tambayoyi.

A cewar wata wasika a hukumance da majiyarmu ta gani mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda ya ce an yi gayyatar ne a karkashin umarnin babban sufeton ‘yan sanda.

Wasikar ta bukaci Sarkin da ya ziyarci shelkwatar hukumar leken asiri da ke Abuja a ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025, da karfe 10:00 na safe.

Idan za a iya tunawa Hukumomin tsaro sun sanya takunkumi kan hawan sallah saboda matsalolin tsaro da kuma yiwuwar tashin hankali.

Duk da haka, an yi zargin cewa Sarki Muhammadu Sanusi ya ci gaba da gudanar da hawan Sallah, inda ya jawo hankulan jama’a da dama da kafafen yada labarai a ranar Sallah da Hawan Nasarawa tare da ziyartar gidan gwamnati.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet