Featured
Gwamnatin Kano Ta Garkame Filin Shaƙatawar Dake Gidan Zoo Saboda Rawar Da Bata Kamata Ba
Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jihar Kano ta rufe wani filin shaƙatawa da ke gidan adana namun daji na Kano (Zoo) bayan an yi zargin shirya wasannin ƙade-ƙade da raye-rayen da suka saɓawa al’ada.
Rufewar ya biyo bayan wani binciken da kwamitin sa ido da shugaban hukumar Abba El-Mustapha ya kafa wanda Daraktan Al’adu Abubakar Zakari Garun Babba ya jagoranta.
An dorawa kwamitin alhakin kula da wuraren shakatawa a lokacin bukukuwan Sallah da aka yi kwanan nan.
A cewar hukumar, lamarin ya shafi rawa tsakani namiji da mace a wani yanayi da ake ganin ya saba wa saba wa al’adun malam bahaushe.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce hukumar ta Hisbah ce ta fara sanar da hukumar tace fina-finai bayan da jami’anta da ke boye a gidan namun dajin suka kai rahoton faruwar lamarin.
An tura jami’an leken asiri na Hisba don tabbatar da tsari da kuma dakile ayyukan da ake ganin ba su da kyau a lokacin bukukuwan.
Bayan tabbatar da rahoton, hukumar ta kama kayan aikin da aka yi amfani da su a filin wasan. Jami’an Hisbah sun tsare matar, yayin da aka ce mutumin ya gudu.
Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai na Kano, Abba El-Mustapha, ya nuna jin dadinsa ga al’ummar Jihar Kano bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin an tabbatar da kyawawan halaye.
Ya kuma mika godiyarsa ga jami’an Hisbah, da ‘yan sanda, da kuma jami’an tsaro na farin kaya (DSS) bisa ci gaba da kokarinsu na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.
