Connect with us

Featured

Sarki Sanusi Ya Nada Sabon Galadima, Wambai, Da Sauran Mukamai A masarautar Kano

Mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya amince da wasu muhimman nade-nade na gargajiya a majalisar masarautar Kano, bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Galadima Kano, Alhaji Abbas Sunusi ya rasu ne a ranar 1 ga watan Afrilu, bayan doguwar jinya.

Sarkin ya nada Alhaji Munir Sanusi a matsayin sabon Galadiman Kano, sarauta mai daraja da marigayi Abbas Sunusi ya rike.

Kafin hawansa, Munir Sanusi ya rike mukamin Wamban Kano kuma Hakimin Bichi.

Sarkin ya kuma daukaka darajar Alhaji Kabiru Tijjani Hashim zuwa Wambai, yayin da Mahmud Ado Bayero ya samu Turakin Kano.

Hakazalika Sarkin ya nada dansa Adam Lamido Sanusi wanda aka fi sani da Ashraf a matsayin sabon Tafidan Kano, yayin da Ahmed Abbas Sanusi dan marigayi Galadima aka nada Yariman Kano.

Wata majiya ta fadar ta tabbatar da nadin ga SolaceBase a ranar Talata, inda ta bayyana cewa hukuncin ya nuna yadda Sarkin ya jajirce wajen ci gaban al’adu, da nagarta da kuma kiyaye al’adun masarautar Kano.

Ana sa ran sabbin masu rike da mukaman da aka nada za su taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari, jagoranci, da kokarin ci gaban al’umma a fadin jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet