Connect with us

Featured

NBC Ta Dakatar Da Eedris Abdulkareem Daga Yaɗa Wakarsa Ta “Tell Your Papa” A Rediyo Da Talabijin

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Kasa NBC ta haramtawa gidajen rediyo da Talabijin na Najeriya yaɗa wakar nan mai taken “Tell Your Papa” ta fitaccen mawakin nan, Eeedris Abdulkareem, inda ta yi nuni da cewa “abin kyama ce.”

A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan Afrilu 9, 2025 kuma mai kula da harkokin yada labarai, Susan Obi ta fitar, ta ce hukumar ta ayyana wakar a matsayin abar ƙin yadawa a karkashin sashe na 3.1.8 na dokar yada labarai ta Najeriya.

Wannan sashe ya hana watsa abubuwan da ake ganin bai dace ba, zagi, ko keta mutuncin jama’a musamman a kafafen watsa labarai na kasa.

A cewar NBC, yayin da waƙar ta sami ƙarfi a dandalin sada zumunta, abubuwan da ke cikin waƙar sun kasa cika ka’idojin yadawa.

Wakar dai mai cike da cece-kuce da aka fitar a farkon makon nan, ta shafi Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, inda ta yi kira gare shi da ya tunkari mahaifinsa kan tabarbarewar yanayin zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya.

A cikin waƙar mai taken “Ka Faɗa wa Babanka,” wanda aka watsa a X (Twitter) a ranar Lahadi, Abdulkareem ya gabatar da wani sako inda ya zana hoton wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta na yau da kullum.

Wakar ta zo ne a matsayin martani ga kalaman Seyi Tinubu a kwanan baya a jihar Adamawa, inda ya bayyana mahaifinsa a matsayin “babban shugaban kasa a tarihin Najeriya.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet