Connect with us

Featured

Yadda Wani Abun Fashewa Ya Tashi Da Ɗan Gwangwan

 

Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar.

Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib Zakiru, da ƙonewar sashin wani gida da ke daura da wajen da ’yan gwangwan ke sana’arsu.

Lamarin ya faru unguwar IdiAraba, ta kuma zanta da mammalakin wajen sana’ar ta ’yan gwangwan, Alhaji Haruna Musa, wanda kuma shi ne shugaban masu sana’ar a yankin, inda ya shaida wa majiyarmu cewa, suna zaune sai suka ji wata irin ƙara mai karfi, ko da suka zo wajen sai suka tarar da wuta ta tashi.

“Da muka zo mun yi ƙoƙarin kashe wutar, da jami’an ’yan sanda suka zo, sun fito da wasu bamabamai na soji guda biyu suka ce daya daga cikin bama-baman ne ya fashe. Wannan ne ya sa suka gayyato ƙwararrun jami’an tsaro a sashen kwance bam, suka zo, suka yi bincike, suka tafi da bama-baman.

 

“Wannan da Allah Ya yi wa cikawa shi ne ya taho da bama-baman kuma yana kokarin fasa guda daga cikinsu ne abun ya tashi, ya halaka shi, wanda zuwan jami’an tsaro ne suka sa aka killace wajen, aka rufe, aka hana mutane shiga, kuma haka ne ya janyo wutar da ba ta mutu ba, ta shafi wani gida da ke gefen wajen, inda ta kone ɗakuna biyar lamarin da ya janyo mutane gidan suka yi asarar kayayyakinsu da kuma mutsuguninsu”, in ji shi.

Haruna Musa ya shaida cewa, mutumin da hadarin ya rutsa da shi magidanci ne kuma ya bar mace guda da ’ya’ya biyu. Haka kuma baya ga shi babu wani da ya jikkata a sakamakon hadarin, ba kamar yadda ake faɗa a wasu jaridu ba cewa, mutum uku sun jikkata. Ya ce tuni aka yi jana’izarsa a bisa jagorancin Sarkin Hausawan IdiAraba, Alhaji Hassan Auyo.

 

“yanzu haka mutanen da wutar ta lalata wa gida ba su da wajen kwana, kuma yawancinsu mata ne zawarawa da tsofaffi da yaransu kanana. Mun yi magana da masu sana’ar gwagwan din domin a gyara masu wajen zamansu. Muna fatan mahukunta sun dubi wannan abu a matsayin hadari ne da ya auku, su kuma ba mu dama mu ci gaba da sana’armu. Muna jan kunnen manbobinmu, su guji kayayyaki masu hadari”, In ji shi.

Wasu mata da suka rasa muhallinsu sakamakon gobarar da ta biyo bayan fashewar bam din. Maman Shahid da wutar ta kone kayan dakinta kurmus, ta shaida wa Aminiya cewa, ‘‘da fari ina kwance a kan gado ne sai karar bam din ta riguzo da rufin silin dakina suka zubo kuma sai na taso na fito daga dakin. Bayan nan kuma

ina zaune a waje ina kokarin yi wa yara abinci sai yaro ya ce, Umma hayaki. Ba mu yi aune ba sai ga wuta ta tashi, ta kone mana dakuna. A lokacin da na yi yunkurin fitar da tukunyar gas din da nake girki, bayan wannan duk kayanmu sun kone, yanzu haka rabe-rabe muke yi wajen da za mu kwanta tare da ‘ya’yanmu”, In ji ta.

Hakazalika, Malama Talatu da ita ma lamarin ya rutsa da ita ta shaida wa Aminiya cewa, tana wajen kasuwancinta na abincin da take dafawa, ta sayar lokacin da labarin ya riske ta, ta ce kayan ta da ke dakin duk sun kone ba su tsira da komai ba sai kayan da ke jikinsu, inda ta mika kokan bara ga mahukunta da masu hannu da shuni domin su taimaka masu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet