Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Wa’adin Wata 14 Domin Kammala Hanyar Abuja-Kaduna-Zaria

Gwamnatin Tarayya ta bai wa Kamfanin Gini na Infiouest wa’adin wata 14 domin kammala sake gina Sashe na II na hanyar Abuja-Kaduna-Zaria mai kudin Naira biliyan 777.

An bai wa Infiouest aikin wannan sashe na biyu a kan farashin Naira biliyan 525 bayan soke kwangilar farko da aka bai wa Kamfanin Julius Berger Plc saboda rashin jituwa kan karin kudi.

Ministan Ayyuka, Engr. David Umahi, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin sashe na biyu a Jere, karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Umahi ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa kokarin gwamnatin tarayya domin tabbatar da kammala aikin cikin lokaci.

Ya bayyana cewa hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano mai tsawon kilomita 700 za ta rage yawan hadurra da kuma cunkoso da ke faruwa da zarar an kammala aikin.

Ministan ya ce, “A karkashin jagorancinka (gwamnan Kaduna), wadannan hanyoyi masu tsawon kilomita 700 za a kammala su, kuma abin farin cikin shi ne za a yi su ne masu matukar inganci.”

“ Muna da sassa guda uku – sashe na 1 yana Abuja, sashe na 3 yana Kano. Sashe na Kano tsakanin Zaria da Kano ya kusa kammaluwa a hannun Julius Berger. Hanyar tana da tsawon kilomita 350, inda Julius Berger ya kammala kilomita 240.

“Kuma Shugaban Kasa ya kara wani tsawon kilomita 11 a bangaren Kano domin kai hanyar zuwa Filin Jirgin Sama na Aminu Kano. Kuma wannan aikin yana gudana yanzu tare da sauran bangaren da ke cikin Jihar Kano.

“Gaba dayan hanyar – shugaban kasa ya bada umarni cewa a sanya fitilun hasken rana a duk tsawon hanyar. Kuma yau, shugaban kasa ya amince da kammala sassan 1 da 3, jimillar kilomita 118 akan kudin Naira biliyan 252.”

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet