Connect with us

Featured

ECOWAS Ta Fara Tattauna Yadda Za Ta Sauya Wa Cibiyoyinta Da Ke Ƙasashen AES Matsugunni

 

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta fara yunkurin sauya wa cibiyoyinta da ke ƙasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso matsugunni, bayan ficewarsu daga cikinta.

A wani taro na musamman na majalisar ministocin ƙungiyar ta ECOWAS ta yi a birnin Accra na Ghana, ministocin sun tattauna kan matakan da za a yi amfani da su wajen ɗauke cibiyoyi da hukumomin ƙungiyar da ke ƙasashen na AES, waɗanda yanzu ke ƙarƙashin mulkin soja.

A jawabinsa ya yin buɗe taron, shugaban majalisar kuma ministan harkokin wajen Najeriya Amb Yusuf Tuggar, ya ce duk da cewa ba shi ne babban batun da ya kamata su tattauna a taron ba, amma ya zame musu wajibi su tattauna inda aka dosa game da makomar cibiyoyinsu.

Ministocin sun kuma tattauna yadda za a tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyuka a cibiyoyi masu muhimmanci na ƙungiyar da suka haɗa da tsaro da tattalin arziki da kuma abinda ya shafi zirga-zirga tsakaninsu.

Haka nan taron majalisar ministocin zai kuma tattauna yadda ECOWAS za ta dakatar da gudanar da ayyukanta a waɗancan ƙasashe uku, da kuma samar da mafita game da ƙalubalen da ka iya bayo bayan ficewar ta su.

Ana sa ran a ƙarshen taron, za a gabatar da cikakken tsari na yadda za a sauya matsugunnin ofisoshin ECOWAS da ayyukasu da ke ƙasashen Uku na AES, zu zuwa wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar na daban.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet