Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Aikin Titi Mai Tsawon Kilomita 5 A Rimin Gado

Zababben shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Alhaji Muhd Sani Salisu Jili, ya kaddamar da aikin gina titi mai tsawon kilomita 5 wanda zai ratsa Dutsen Gambori, Bankamawa, Sauna, Yangu har zuwa Doka Dawa. Wannan aiki wani bangare ne na sauƙaƙa zirga-zirga, farfaɗo da kasuwanci da kuma inganta rayuwar al’umma a karamar hukumar.

Shugaban ya bayyana cewa aikin wani ɓangare ne na haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf. Ya tabbatar da cewa aikin zai kammala cikin lokaci, tare da amfani da ingantattun kayan aiki. Haka kuma, ya ce aikin ya buɗe damar aiki ga matasa da mazauna yankin, wanda hakan zai rage zaman banza da ƙara walwala.

Ya ƙara da cewa ana shirin fara wani sabon aikin titi mai tsawon kilomita 5 a garuruwan Sauna, Na Zaki, Kazar Dawa ya Fito ta Doka Dawa, domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a fadin karamar hukumar.

A nasa jawabin, Sakataren Mulki kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar, Alhaji Sale Adamu, ya bayyana jin daɗinsa da wannan ci gaba. Ya yaba wa kokarin shugaban karamar hukumar da kuma gwamnatin jihar, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da yi masa addu’a.

Daga bangaren al’umma, Isiyaku Mati, ɗan asalin mazabar Zango G7, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan aiki. Ya ce: Gwamna da shugaban karamar hukumar sun tabbatar da cewa suna tare da talakawa. Wannan titi zai taimaka sosai wajen sauƙaƙa mana hanya da bunƙasa sana’o’inmu.”

Shi ma Safiyanu Mai Sassabe da- Rido ya nuna godiyarsa ga shugaban karamar hukumar da Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya ce: “Ba mu yi zaben tumun dare ba. Wannan aiki alama ce ta gaskiya da aiki ba kawai alkawari ba.

Sa hannu:
Arribbabatu Sani Yakasai
Jami’ar Yada Labarai
Karamar Hukumar Rimin Gado

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet