Connect with us

Featured

Atiku Ya Bukaci Tinubu Da Ya Janye Iyalansa Daga Shiga Harkokin Gwamnati

Ɗan takarar shugabancin ƙasar nan, Atiku Abubakar, ya ce ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya janye iyalansa daga shiga harkokin gwamnatin ƙasar.

Wata sanarwa da Atiku Abubakar din ya fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan al’amuran yaɗa labarai Paul Ibe, ta ce, ɗa ga shugaban Kasa, wato Sheyi Tinubu wanda ke kokarin nemarwa mahaifinsa magoya baya ko ta halin ƙaƙa, na kokarin amfani da kujerar mahaifinsa wajen sanya shakku a zukatan jama’ar ƙasar.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa, wannan tsari da Sheyi Tinubu ya runguma, shakka babu, ba zai haifar da ɗa mai idanu ba.

Sanarwar ta ce, zargin da shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS, wato Atiku Isah ya yi, kan yunƙurin yin garkuwa da shi, bisa umarnin Sheyi Tinubu abin damuwa ne sosai.

Wannan zargi da ake yiwa ɗan shugaban na Najeriya ya haifar da fargaba a zuƙatan ‘yan ƙasa da dama, la’akari da irin girman kujerar mahaifinsa, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma yi watsi da zargin da ake yiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, na haɗa kai da shugaban na NANS, Kwamred Isah wajen cimma wasu manufofi na siyasa, tare da shiryawa gwamnati mai ci bita da ƙulli.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet