Featured
ISMPH ta horar da Ƴan Jarida kan yaki da mutuwar mata masu juna biyu a jihar Kano
Kungiyar Kasa da Kasa ta Harkokin Yada Labarai a Fannin Lafiya (ISMPH) ta horas da ‘yan jarida 25 a Kano, inda ta ba su kwarewa da karin ilimin da zai taimaka wajen wayar da kan al’umma kan harkokin lafiya da rage mace-macen mata masu juna biyu tare da inganta samun damar kula da lafiya a fadin jihar.
Wannan horo na uku ya hada ‘yan jarida, kwararru a fannin lafiya , da jami’an gwamnati domin tattauna kalubalen yada labaran lafiya da samar da mafita tare.
Solomon Dogo, Daraktan Shirye-shirye na
ISMPH, ya bayyana dalilan da suka sa aka shirya wannan horo na musamman da nufin inganta yadda kafafen yada labarai ke rufe batutuwan da suka shafi lafiya a Jihar Kano.
Wannan shiri da EngenderHealth ta dauki nauyinsa a Najeriya, ya horas da ‘yan jarida 25 kan bangarorin lafiya masu muhimmanci da za su taimaka wajen rage yawaitar mace-macen mata masu ciki a yankin.
Dogo ya bayyana cewa ISMPH tana da dogon tarihi wajen aiki da ‘yan jarida don inganta dabarunsu, musamman a fannin rahotannin lafiya. Ya jaddada rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen yada bayanan lafiya zuwa matakin kasa, don tabbatar da cewa al’umma na da cikakken bayani kan tsare-tsaren gwamnati da suka shafe su.
“Wannan horo yana da matukar muhimmanci domin yana mayar da hankali kan bangarori kamar RMNCAH (lafiyar haihuwa, yara kanana, jarirai, da matasa), sabon tsarin SWAp (sector-wide approach), da tsarin inshorar lafiya.
Wadannan su ne fannonin da ke bukatar kafafen yada labarai su isar da sahihan bayanai cikin lokaci da tasiri ga jama’a, musamman kan sabbin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ke kawo wa,” a cewar Dogo.
Daya daga cikin mahimman batutuwan da aka mayar da hankali a kai shi ne wayar da kai kan tsarin inshorar da lafiya da amfaninsa. Wannan tsarin yana ba mata tallafin kudin haihuwa, ciki har da tiyatar haihuwa (C-section), da sauran ayyukan lafiya da suka zama dole. Wannan tallafi na nufin rage matsin lambar kudi da mata ke fuskanta, tare da tabbatar da samun ingantacciyar kulawa
Baya ga tsarin inshorar lafiya, shirin SWAp na karfafa hadin gwiwa tsakanin abokan hulda domin tara albarkatu da aiwatar da ayyuka da nufin inganta harkar kiwon lafiya da rage mace-macen mata.
Dogo ya jaddada cewa wadannan kokari sun fi dacewa a Jihar Kano wadda ke daga cikin jihohin da ke da mafi yawan mace-macen mata masu ciki a Najeriya.
“Idan aka aiwatar da wadannan tsare-tsare gaba daya, za su shafi muhimman abubuwan da ke haddasa mace-macen mata a Kano. Ta hanyar horas da ‘yan jarida, muna basu damar isar da wadannan sauye-sauyen yadda ya kamata, domin tabbatar da cewa bayanin ya isa ga wadanda suka fi bukatarsa,” in ji shi.
Da yake jawabi ga mahalarta, Kwamishinan Lafiya na Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana muhimmancin kafafen yada labarai a harkar sadarwa ta lafiya.
“Na yi matukar farin ciki da kasancewa cikin wannan horo. Ina da yakinin muhimmancin sanar da masu yada labarai. Kafafen yada labarai na da tasiri sosai, kuma jama’a na yarda da rahotonsu ba tare da bincike ba. Wannan ne ya sa dole mu hada kai da su don tabbatar da sun fahimci dukkan bayanan da suke yada wa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Gidan yada labarai na iya kawo zaman lafiya ko tayar da hankali cikin sa’o’i 24 kacal. Wannan yana nuna nauyin da ke kan yan jarida wajen tabbatar da zaman lafiya da karfafa tsarin rayuwar al’umma.
A yau, mun mayar da hankali kan lafiya—musamman RMNCAH, kudaden lafiya, lafiyar jarirai, da tsarin SWAp—wadanda duk suna da mahimmanci wajen inganta lafiyarmu.”
Shima a jawabin da ya gabatar a madadin Daraktan EngenderHealth na kasa, Dr. Kabiru Atta ya karfafa gwiwar mahalarta da su aiwatar da abin da suka koya a horon.
“Bangaren lafiya yana da matukar muhimmanci, kuma muna da kudurin ci gaba da aiki kafada da kafada da ‘yan jarida domin haskaka nasarorin da aka samu da wallafa jaridu masu dauke da gudunmawar kafafen yada labarai wajen inganta harkar kiwon lafiya,” in ji shi.
