Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kudurin Karba-Karba A Tsarin Shugabancin Najeriya

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi watsi da wani kudiri da ke neman sauya kundin tsarin mulki na 1999 domin tabbatar da tsarin karba-karba a mukamin Shugaban Kasa da Mataimakin sa a tsakanin yankuna shida na Najeriya (Arewa ta Tsakiya, Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma, Kudu Maso Gabas, Kudu Maso Kudu, da Kudu Maso Yamma).

Kudirin, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu ya gabatar, mai taken “Kudirin Doka don Sauya Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, Cap. C23, Dokokin Tarayyar Najeriya na shekarar 2004, domin samar da tsarin karba-karba a mukaman Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa a tsakanin shiyyoyi guda shida na kasar nan, wato: Arewa ta Tsakiya, Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma, Kudu Maso Gabas, Kudu Maso Kudu, da Kudu Maso Yamma, da kuma sauran batutuwan da suka shafi hakan (HB. 2291).”

Yayin tattaunawa a zaman majalisar, wasu ‘yan majalisa kamar su Aliyu Madaki (NNPP, Kano), Sada Soli (APC, Katsina), da Bello El-Rufai (APC, Kaduna) sun soki kudirin, inda suka bayyana tsarin a matsayin saɓa ƙa’ida da kawo rarrabuwar kan yan ƙasa.

Sai dai wasu yan majalisar kamar Ali Isah (PDP, Gombe) sun goyi bayan kudirin, inda suka ce zai kawo adalci da haɗin kan ƙasa.

Daga ƙarshe, bayan muhawara mai zafi, mafi yawan ‘yan majalisa sun kada kuri’ar kin amincewa da kudirin, wanda hakan ya sa Mataimakin Kakakin Majalisar ya tabbatar da cewa kudirin bai samu karbuwa ba.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet