Connect with us

Featured

Rahotanni Na Bayyana Cewa Sojojin Nijar Sun Yi Wa Jagororinsu Bore

Har yanzu babu cikakken bayani daga barikin sojojin Termit na Jamhuriyar Nijar, inda bayanai ke cewa sojoji sun yi wa shugabanninsu bore tare da bijire wa doka.

Yunƙurin na sojoji ya kawo yamutsi a tsarin shugabanci na barikin, yayin da sojojin ke ƙokarin afka wa shugananni.

Tun ranar 8 ga watan da muke ciki ne, bayanai ke cewa an samu yamusti tsakanin sojoji a barikin, yayin da ƙananan suka yi bore tare da bijire wa shugabanninsu.

Rahotanni sun fayyace cewa sojojin na wannan bore ne bayan da aka jibge su a barikin da ke cikin sahara, abin da ya raba su da cikin gari, da ku wata alaƙa da suke da ita da iyalai da ƴan uwa.

Baya ga wannan kuma, akwai tsananin cututtuka da ke da alaƙa da yunwa da sojojin ke fama da su, da kuma rashin kayan aiki yayin da ake fama da barazanar tsaro, da jan ƙafa wajen biyan su haƙƙoƙinsu.

Sakamakon nisan da barikin ke da shi da cikin gari, bayanai sun ce an kwashe sama da kwanaki 4 ana boren, ba tare da an sani a cikin gari ba.

Da ma masu sanya idanu kan harkokin tsaro, sun jima suna kira ga hukumomi da su duba halin da barikin da kuma sojojin ke ciki, yayin da suke hasashen hakan ka iya faruwa.

Sai dai wasu bayanai da babu tabbaci a kansu, sun ce an kama kwamandan barikin, sa’o’i kaɗan bayan boren.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet