Connect with us

Featured

NDLEA Ta Kama Wani Tsoho Mai Shekaru 80 Dauke Da Miyagun Kwayoyi

Hukumar NDLEA da ke hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Kasa ta ce jami’anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi.

A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa.

Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024.

“Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Sunday mai shekara 82 da ƴarta mai shekara 32 mai suna Chisom Uchechi a jihar Abia da miyagun ƙwayoyi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet