Connect with us

Featured

Dalilin Da Ya Sa Gwamna Zulum Kwana A Marte Bayan Harin Boko Haram

Gwamnan Jihar Borno da ke Najeriya, Babagana Umara Zulum ya ce ya je garin Marte ya kwana ne domin ƙarfafa wa jama’ar garin gwiwar ci gaba da zama a cikinsa, sakamakon kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai a makon jiya.

Zulum wanda ya bayyana cewar aƙalla mutane 20,000 suka gudu daga garin domin tsira da rayukansu, ya ƙara da cewar ba za su taɓa barin garin ya faɗa hannun ƴanta’addan ba.

Gwamnan ya kuma ce aƙalla garuruwa 300 da ke yankin suka tashi saboda hare-haren ƴan ta’addan, saboda haka gwamnatiinsa ke ɗaukar matakan da suka dace tare da jami’an tsaro domin kare lafiya da dukiyoyin mutanen Marte.

Zulum ya ce daga cikin matakan da suka ɗauka na kare Marte da kuma wasu garuruwan da ke yankin, har da girke jami’an Sakai waɗanda aka horar da su, baya ga jami’an tsaron soji da ƴansanda.

Gwamnan ya kuma buƙaci taimakon gwamnatin tarayya domin tinkarar wannan matsala, musamman la’akari da yadda hare-haren mayaƙan suka karu a wannan lokaci.

Jihar Borno na ci gaba da fuskantar ƙarin hare-hare Boko Haram, musamman a ƴan kwanakin da suka gabata.

A makon jiya kawai, mayaƙan sun kai hare-hare aƙalla sau 6 a garuruwa daban daban, wanda ya ritsa da jami’an soji da kuma fararen hula.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet